Pantami ya nada Nuhu Abdullahi a matsayin jakada

0
126

 

Ministan Sadarwa da tattalin arziki na zamani,Ali Isa Pantami ya nada Abdullahi Nuhu wanda a ka fi sani da Mahmoud a fim din Labarina, a matsayin jakada.

Minista Pantami ya nada jarumin fina-finan Kannywood din ne a matsayin jakadan katin shaidar dan kasa a karkashin Hukumar Ba da Shaidar Dan Kasa ta Najeriya [NIMC].

Sanarwar nadin na kunshe ne a cikin takarda da hukumar NIMC ta aika wa jarumin a farkon makon nan.

A cikin ayyukan da zai gudanar a wannan matsayi shi ne jagorantar fadakarwa da wayar da kan jama’a kan muhimmancin mallakar shaidar dan kasa da tsare-tsaren gwamnati kan shaidar zama dan kasa da kuma alfanunsa.

Jarumin zai kuma halarci duk tarukan wayar da kai a bainar jama’a da hukumar ta shirya, da kuma ta kafofin yada labarai kan muhimmancin mallakar shaidar dan kasa, da sauran shirye-shiryen na fadakarwa.

Nadin na shekara guda ne, kuma ya soma aiki tun ranar 16 ga watan Satumba da muke ciki.

Abdullahi Nuhu ya dade yana fitowa a fina-finan Kannywood, kuma fin din da ya fara tashe shi ne shirin mai dogon zango na Labarina, a inda ya fito a Mahmoud.