Farashin danyen mai ya fadi wanwar a kasuwar duniya

0
101

Farashin danyen mai a kasuwar duniya ya fadi a ranar Juma’a, 23 ga watan Satumba yayinda Najeriya ke fama da satar danyen mai dake gudana a kudancin kasar.

Wannan shine faduwa mafi muni da farashin man yayi cikin watanni tara da suka gabata.

Hakazalika rahoton MSCI ya nuna cewa a ranar Juma’a Dalar Amurka ta yi tsadar da bata taba yi ba cikin shekaru 20.

Bugu da kari, Fam (£) na birtaniya ya yi irin faduwar da bai taba yi ba cikin shekaru 37 yayinda sabon ministan kudin Birtaniya, Kwasi Kwarteng, ya sanar da karban basussuka da yafewa mutane wasu kudaden haraji.

(Legit)