Shugaban Nigeria Bola Tinubu, ya nuna takaici akan yadda mayakan boko haram suka kashe sojojin kasar a wani harin da suka kaiwa sansanin su a karamar hukumar Damboa, ta Borno.
Sansanin da aka kaiwa harin ya kasance a kauyen sabon Gida.
:::Wutar daji ta kashe mutane 5 da kone gidaje dubu 2 a birnin Los Angeles na Amurka
Cikin wata sanarwa da fadar gwamnatin ƙasar ta fitar, ta ce Tinubu ya jajanta wa rundunar soji sakamakon mutuwar dakarunta shida a harin.
Cikin sanarwar fadar shugaban kasar, Tinubu ya nemi a gabatar da cikakken bincike don sanin abun da ya haddasa kai harin da kuma umarnin hana sake faruwar harin nan gaba.
A ranar Asabar data gabata ne mayaƙan Boko Haram bangaren ISWAP suka ƙaddamar da harin da asubahi akan sansanin sojin lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar sojoji 6 da mayaƙan Boko Haram da suka zarce 30.
Tinubu, yace tabbas sojoji sun yi gagarumin kokarin da yakai ga nasarar dakile harin wanda hakan yasa mayakan boko haram basu cimma nasarar da suke nema ba.