Shugaba Tinubu ya amince a kara kudin kiran waya dana Data

0
33

Shugaba Bola Tinubu, ta hannun Ministan sadarwa Dr. Bosun Tijani ya ce nan ba da jimawa ba za a kara kudin kiran waya dana Data.

Sai dai yace ba da kashi 100 za’a kara kudin ba kamar yadda kwamfanonin sadarwar na GLO, MTN, Airtel, da 9mobile, suka bukata ba.

Tijani ya ce ana ci gaba da tuntubar juna da tattaunawa kan batun Karin kuÉ—in sadarwar da suka hada da kuÉ—in kira da kuma Data.

Wadanda suka halarci taron sun hadar da wakilan gwamnatin tarayya na hukumar NCC, NITDA, da kuma kungiyar masu kamfanonin sadarwar kasar nan baki daya.

Haka shine yake tabbatar da cewa nan gaba kadan al’umma zasu kara fuskantar wani harajin a fannin sadarwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here