Nigeria ta karbo bashin Dala miliyan 254.76 daga kasar China

0
48

Bankin cigaba na kasar China ya sahale a bawa Nigeria bashin dala miliyan 254.76, don taimakawa a samu damar kammala aikin gina titin jirgin kasan daya taso daga Kano zuwa Kaduna.

Bayar da bashin yazo yan kwanaki kadan gabanin ziyarar ministan harkokin wajen China, Wang Yi, zuwa nahiyar Afrika, da a yau laraba, ake sa ran Wang Yi, zai sauka a Nigeria, don tattaunawa da shugaban kasa Tinubu, a ranar alhamis, kamar yadda ma’aikatar harkokin wajen kasar nan ta sanar.

:::Gwamnatin Kaduna zata dasa bishiyu miliyan 10 saboda yakar sauyin yanayi

Aikin gina titin jirgin kasan na Kano zuwa Kaduna, ya kasance mai nisan kilomita 126, wanda aka kiyasta kwangilar sa akan kudi dala miliyan 973, kuma yake fuskantar koma baya saboda rashin isassun kudaden da za’a kammala aikin.

Bankin cigaban China, yace bayar da bashin zai taimaka a kai ga kammala aikin titin cikin sauki, sannan ana kyautata zaton da zarar an gama titin zai taimakawa sifurin al’umma, da karuwar tattalin arziki.

Dama wani kamfanin kasar China, shi aka bawa aikin samar da titin tun a baya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here