Auren G-fresh da Alpha Charles yana tangal-tangal

0
26

Jarumin Tiktok G-Fresh ya ce aurensu da Alpha Charles na tangal-tangal.

A kwanakin baya G-fresh yace masu shirin zuwa bikin nasu su dakata har sai sun yi gwajin genotype, tsakanin sa da masoyiyar sa Alpha Charles.
Tun kafin yanzu ma’abota shafukan sada zumunta sun sha bayyana ra’ayoyin su akan auren na G-fresh, musamman yanda aka ganshi yana yin ma’amala da Alpha Charles, kamar tun tuni sun yi aure.
Auren G-fresh dai zama wani abun cece-kuce a kafafen sada zumunta, sakamakon cewa duk lokacin da zai yi aure sai an samu wani abu da zai kawo bayyana ra’ayoyin al’umma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here