Shugaban Ukraine yana son Trump ya kawo karshen yakin su da Rasha

0
41

Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky yace shugaban Amurka mai jiran gado Donald Trump, ne kaɗai zai iya bayar da tabbacin samar da tsaron da zai iya kaiwa ga kawo ƙarshen yakin da ƙasar sa ke yi da Rasha.

A wata hira da aka yi da shi, Mista Zelensky ya yaba da tasirin shugaban Amurkan mai jiran gado, ya kuma yi nuni da cewa yana da damar da zai iya dakatar da mamayar da Rasha ke ci gaba da yi Ukraine.

Hakan yazo bayan da Trump ya yi alƙawarin kawo ƙarshen yaƙin cikin gaggawa, ba tare da bayar da cikakken bayanin matakan da zai ɗauka ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here