PDP ta sha alwashin samun karin kujerun gwamnoni a shekarar 2027

0
74

Shugabancin jam’iyyar PDP a matakin kasa yasha alwashin samar da karin gwamnonin da jam’iyyar ke dasu tare da karbar mulkin Nigeria a shekarar 2027.

Shugabannin jam’iyyar ne suka sha alwashin a jiya lahadi lokacin da suka ziyarci gwamnan jihar Bayelsa, Douye Diri, a mahaifiyar sa ta Sampou, dake karamar hukumar Kolokuma/Opokuma.

PDP tace zata samu karin gwamnoni akan 12 da take dasu a halin yanzu in har lokacin zaben shekarar 2027, ya zo.

Ma’ajin kudin jam’iyyar PDP Ahmad Yayere, wanda yayi magana a madadin shugabannin jam’iyyar yace, zasu samu nasara musamman akan yadda al’umma suka shiga halin kuncin rayuwa saboda gwamnati mai ci, yana mai cewa PDP ce kadai zata iya kwace mulki daga hannun APC.

A cewar sa yan jam’iyyar APC ba zasu samu damar fita yakin neman zabe ba, saboda yan Nigeria zasu iya jifan su da duwatsu sakamakon kuncin rayuwa da suke ciki.

Da yake nasa jawabin gwamnan jihar Bayelsa Douye Diri, cewa yayi dole sai PDP da gwamnonin ta sun hada kai don cimma burin dake gaban su, yana mai tabbatar da cewa hakan ne kadai zai basu nasara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here