Zamu yi adalci ga masu gidajen da aikin gadar Tal’udu ya shafa—Gwamnan Kano

1
56
Abba Gida-Gida
Abba Gida-Gida

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, yayi alkawarin yin adalci wajen biyan diyya ga wadanda za’a tasa daga matsugunan su biyo bayan aikin samar da gada a shataletalen Tal’udu, dake birnin Kano.

Bayanin gwamnan ya shafi masu gidaje, da sauran kadarori a guraren da za’a iya rushewa saboda samun nasarar aikin gina gadar, wadda ake kan ginawa a yanzu haka.

Gwamnan Kano, ya sanar da hakan lokacin da yake zantawa da jagororin al’ummar yankin, da masu ruwa da tsaki.

A cewar sa, gwamnatin ta fahimci rashin jin dadin da wadanda aikin ya shafa suke ciki, yana mai cewa za’a tabbatar da adalci gurin biyan duk wanda aikin ya shafa diyya zuwa asusun bankin kowa kai tsaye don kawar da dannewa wasu hakkin su, da kuma yin komai a bayyane.

Bugu da kari zamu bawa wadanda abin ya shafa filaye kyauta don ginawa su cigaba da rayuwa, inji gwamnan Kano.

Alhaji Abba Aminu Imam, shine shugaban kwamitin al’ummar Tal’udu, da suka gana da gwamnan jihar Kano, inda ya bayyana cewa sun ji dadin bayanan da gwamnan yayi, yana mai cewa akwai bukatar a yi kokarin biyan diyyar akan lokaci.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here