Yan sanda 140 na birnin Abuja sun mutu a shekarar 2024

0
52

Rundunar yan sandan kasa, tace jami’an ta 140, masu aiki a birnin tarayya Abuja ne suka mutu a shekarar 2024, data gabata.

Kwamashinan ‘yan sanda na birnin Abuja, Olatunji Rilwan Disu ya ce daga cikin dalilan da suka jawo mutuwar tasu akwai haduwa da suka rika samu da ‘yan Æ™ungiyar IMN ta ‘yan Shi’a a babban birnin.

Kwamashinan ya ce a cikin wadanda suka rasu akwai jami’an da suka kwanta barci basu sake tashi ba.

A cewar sa, an biya wasu daga cikin iyalan dakarun haƙƙoÆ™insu, bisa umarnin babban sufeton ‘yan sanda Kayode Egbetokun.

Daga bisa ni yace rundunar yan sandan Nigeria reshen Abuja, ta samu nasara mai yawa wajen dakile munanan ayyuka a shekarar ta 2025.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here