Farashin man fetur zai sake karyewa a Nigeria—Dillalan Fetur

0
81
man fetur
man fetur

Kungiyar dillalan man fetur masu zaman kansu ta kasa IPMAN, tace aikin da matatar man fetur ta Warri, ta fara yi zai sake karya farashin man fetur a Nigeria.

A kwanakin baya ne matatar man fetur ta Dangote ta rage farashin man man ga yan kasuwa zuwa 899.50, don saukakawa mutane suyi bukukuwan kirsimeti da sabuwar shekara a sauki, wanda shima kamfanin NNPCL ya sanar da rage nasa farashin zuwa 899.

Daga wancan lokaci ne dillalan man suka ce za’a fara siyar da man a kudin da bai kai naira 950, amma har yanzu akwai gidajen mai dake siyar da litar akan farashin daya zarce wanda IPMAN ta alkawarta.

Tuni dai aka ce matatar Warri, ta fara tace man Diesel da kalanzir.

Babban jami’in IPMAN, Alhaji Zarma Mustapha, ya ce aikin matatar Warri da matatar Fatakwal zai taimaka wajen rage tsadar fetur da wadatar sa a Nigeria.

Shugaban NNPCL, Mallam Mele Kyari, ya tabbatar da cewa matatun Fatakwal da Kaduna su ma suna kan aiki, kuma ana sa ran za su fara samar da mai nan ba da jimawa ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here