Ku fara warware matsalar cikin ku kafin ku ceto ‘yan Najeriya – Keyamo ga PDP

0
115

Karamin Ministan kwadago da aikin yi, Festus Keyamo, ya zundi jam’iyyar PDP kan rikicin da ke addabar jam’iyyar.

Keyamo ya ce jam’iyyar ta kasa shawo kan matsalolinta amma a kullum cewa take tana son ceto ‘yan Najeriya.

Wannan na zuwa me tsaka da lokacin da tsagin Gwamna Wike na jihar Ribas a ranar Laraba suka fice daga tawagar kamfen din PDP na kujerar shugaban kasa inda suka jaddada cewa Iyorchia Ayu yayi murabus kafin su shiga tawagar kamfen din.

Keyamo yayi mamakin yadda ‘dan takarar jam’iyyar PDP Atiku Abubakar da PDP ke ikirarin zasu ceto kasar yayin da suka kasa shawo kan matsalar cikin jam’iyyar da wuri.

A wallafar da Keyamo yayi yace : “Jam’iyyar PDP dake cikin rikici saboda yadda ta kasa shawo kan matsalar da inuwar lema ke tattarowa kowacce rana da kuma abu na farko da suke fadin cewa zasu ceto Najeriya; kamar matashin da kafarsa ta kasa kaiwa kuloch din motar dake kokarin shiga gaban tirela! Wannan abu kamar sihri!”