Kamfanin NNPCL yace an gyara matatar fetur ta Warri

0
52

Kamfanin mai na Nigeria NNPCL ya sanar da cewa kawo wannan lokaci sun gyara matatar danyen man fetur ta Warri dake jihar Delta, yana mai cewa a yanzu haka matatar ta kama aiki.

Shugaban kamfanin man Mele Kyari ne ya sanar da haka a ranar Litinin yayin wani taron manema labarai da ya gudanar a matatar, da aka ce zata rika tace gangar danyen mai 125,000 a kowacce rana.

Kyari, yace ba’a kai ga kammala gyara matatar gaba daya ba, amma dai ta fara yin aiki tare da cewa za’a cigaba da gyarata zuwa a kammala gyaran baki daya.

Kyari, yace wasu daga cikin yan Nigeria basa amincewa da batun gyara matatun da suke yi, inda yace amma a yanzu sun nunawa kowa gaskiyar su akan gyaran.

Matatar da ke yankin Ekpan na Warri, an ƙaddamar da ita a shekarar 1978 domin samar da mai ga jihohin kudancin Najeriya bisa kulawar kamfanin NNPCL .

A cewar mai magana da yawun NNPCL, Olufemi Soneye, an tsara kammala aikin ne tun cikin wata ukun farko na 2024.

A watan Nuwamban da ya gabata ne NNPCL ya ce ya kammala gyaran tsohuwar matatar mai ta Fatakwal, wadda ita ma wasu ke cewa babu gaskiya a batun gyrana nata, inda ake zargin cewa a halin yanzu ma matatar ta Fatakwal, bata yin aiki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here