Kamfanin mai na kasa NNPCL yace shugaban kasa Bola Tinubu, baya yi musu katsalandan a harkokin su na yau da kullum.
Baya ga wannan NNPCL yace ba’a nuna wariyar addini, kabilanci, ko siyasa wajen daukar ma’aikata, karin girman ma’aikatan sa da sauran su.
Shugaban sashin sadarwar kamfanin NNPCL, Olufemi Soneye, ne ya sanar da hakan a yau asabar, lokacin da yake mayar da martani akan wata mujallar da Farfesa Farooq Kperogi, ya wallafa, wanda a cikin littafin ya zayyano yadda tsohon shugaban Nigeria Buhari, da Kuma Tinubu, suka taka rawa a al’amuran NNPC.
Soneye, yace kamfanin NNPCL, yana gudanar da ayyukan sa bisa duba cancanta da sanin ya kamata.
Kperogi, yace Tinubu, ya mayar da kamfanin NNPCL tamkar mallakin yarabawa, wanda kabilar yarabawan ke rike da manyan mukamai a kamfanin.
Sai dai shugaban sashin yada labaranKperogi na NNPCL, ya bayyana abubuwan da Kperogi, ya zayyano a matsayin wanda ba gaskiya ba.