Kotu ta yanke hukuncin kisa akan wanda ya kashe mutane 35 da mota a China

0
46

Wata Kotun kasar China ta yanke hukuncin kisa akan wani mutum daya kashe mutane 35 a birnin Zhuhai, ta hanyar kai musu hari lokacin da yake tuka mota.

Wata kafar yada labarai ta kasar ta ce an yanke hukuncin a yau juma’a, akan Fan Weiqiu, mai shekaru 61, da aka tabbatar da cewa ya kashe mutanen da ganganci, lokacin da yake tuka motar atisaye.

Lamarin ya afku a watan daya gabata, wanda Kuma shine kisan mutane da mota mafi muni a China, tun bayan makamancin sa da aka gani a shekarar 2014.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here