Gwamnatin tarayya zata ciyar da dalibai abincin naira biliyan 100 a shekarar 2025

0
53

Gwamnatin tarayya ta shirya kashe naira biliyan 100 wajen ciyar da dalibai abinci yayin da suke daukar darasi a makarantun Firamaren gwamnatin Nigeria a shekarar 2025.

Daily trust, tace an samu bayanin hakan cikin kasafin shekara mai kamawa, da za’a yi aikin ciyarwar karkashin tsarin ma’aikatar kasafi da tsare tsare.

Idan za’a iya tunawa an dakatar da tsarin ciyarwar a watan Junairu, bayan da aka dakatar da shugabar shirin Halima Shehu, saboda zargin almundahana.

Bayan haka a watan Ogusta, ne ministan kudi Wale Edun, yace suna yin shirin dawo da tsarin ciyarwar.

Edun, ya bayar da tabbacin cewa gwamnatin tarayya zata bayar da duk abubuwan da ake bukata don samun nasara a tsarin ciyarwar domin inganta harkokin ilimi da bawa yan Nigeria ilimi mai nagarta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here