Yan Nigeria zasu ji dadi a shekarar 2025—Ganduje

0
68

Shugaban jam’iyyar APC na Æ™asa Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya bawa yan Nigeria tabbacin cewa zasu samu saukin rayuwa a cikin shekarar 2025, yana mai cewa tattalin arzikin kasar zai inganta a shekarar.

Bayan haka, Abdullahi Umar Ganduje ya yi kira ga yan kasa su cigaba da yin haƙuri da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu duk da yanayin da ƙasar ke ciki na kunci.

Ganduje ya bayyana haka ne a saƙonsa na Kirsimeti, wanda sakataren yada labaransa, Edwin Olofu, ya fitar.

A cewar Ganduje, yan Nigeria zasu yi farin ciki domin tattalin arzikin ƙasar zai inganta.

Shugaban APC, ya kara da cewa za’a samu sauki musamman akan wahalhalun da manufofin gwamnatin Tinubu, suka jefa yan Nigeria da ake cewa ana yin su don farfado da tattalin arzikin kasa.

A fannin tsaro, Ganduje yace an fara samun nasara a sakamakon rage yawan yan ta’adda.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here