Samar da wuta a filin jirgin saman Abuja ya lakume naira biliyan 8.73 a shekarar 2024

0
64

Gwamnatin tarayya ta kashe kudaden da yawan su yakai naira biliyan 8.73, wajen samar da tsayayyiyar wutar lantarki a filin tashi da saukar jiragen saman kasa da kasa na Nnamdi Azikiwe, dake birnin tarayya Abuja a cikin shekarar 2024.

Jaridar Punch, ce ta samu jadawalin kashe Kudaden cikin rahoton cibiyar BudgIT, wanda take fitarwa akan kashe kudaden gwamnati.

Rahoton, yace ana samun daukewar wutar lantarki a filin tashi da saukar jiragen, wanda hakan ke haifar da koma bayan harkokin sifurin jiragen sama a Abuja.

Sai dai duk da kashe manyan kudaden har yanzu ana iya fuskantar daukewar wutar lantarki a filin jirgin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here