Al’ummar Yakasai, Rimi da Kofar Mata, sun gudanar da taron neman mafita akan matsalar matasa masu harkar daba a unguwannin.
Taron ya gudana tsakanin dattawan unguwannin da matasan dake yin wannan aiki na Daba, wanda aka gudanar a ofishin kwamishinan ayyuka na musamman na jihar Kano.
Dattawan da suka halarci taron sun dauki alkawarin taimakawa yan daban don komawa yin rayuwa mai inganci kamar sauran mutane.
A nasu bangaren suma matasan da suke yin harkar dabar sun sha alwashin yin zaman lafiya.
Rikicin daba dai yayi kamari a wadannan unguwanni inda hakan ke haifar da jikkata al’umma da kuma asarar rayuka a wasu lokutan.