Ba zamu yi sulhu da yan ta’adda ba—Gwamnan Zamfara

0
138

Gwamnatin Zamfara tace har yanzu tana kan bakanta na yin watsi da batun yin sulhu tsakanin ta da yan bindigar dake addabar Jihar.

Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal Dare, shine ya sanar da hakan, yayin zantawarsa da BBC.

Gwamnan ya ce ya ɗauki wannan matsaya ce ganin cewa a baya an yi sulhu da ‘yan bindigar, amma ba sa mutunta alƙawurran da aka yi da su.

Dare, yace an yi sulhun nan a baya ba sau ɗaya ba, ba sau biyu ba, amma an kasa cimma ake abin da ake so.

Sai dai ya ce duk da haka, ƙofa a buɗe take ga ƴan fashin da ke neman hanyar da za su dawo su rungumi zaman lafiya, ta hanyar miƙa wuya ga hukuma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here