Wanda ya yiwa matar sa fyade zai shafe shekaru 20 a gidan yari

0
64

Kotun kasar Faransa ta samu Dominique Pelico, wanda ya shirya yiwa matar sa fyade da laifi tare da yanke masa hukuncin zaman gidan yari na shekaru 20.

An samu mutumin da laifin shirya yadda ake yiwa matar tasa mai suna Gisele, fyade bayan ya bata kayan saka maye tasha.

Pelico ya shafe fiye da shekara 10 yana shirya yadda maza suke yi wa matarsa, Gisele Pelicot fyaÉ—e.

Kotun ta samu mutane 51 da ake zargin da aikata fyaÉ—en da laifi kuma ta yanke masu hukuncin É—auri a gidan yari na tsawon shekara uku zuwa 15.

Mutanen da suka halarci zaman kotun sun yi kukan jin yadda mijin Gisele, ya aikata mata wannan mummunan aiki da bai yi kama da hankali ba.

Bayan yanke hukunci an samu farin ciki daga mutane, duk da cewa lauyan mijin yayi jawabin cewa akwai yiwuwar su daukaka kara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here