Yan majalisa zasu bawa yan Nigeria rabin albashin su suboda cire tallafin Fetur

0
82

A ranar 31 ga watan Disamba da muke ciki ake sa ran mambobin majalisar wakilai zasu gabatar da kudi naira miliyan N704.91, ga shugaban kasa Tinubu, don taimakawa yan Nigeria matalauta da suke fuskantar matsalolin tattalin arziki saboda cire tallafin fetur.

Idan ana iya tunawa a ranar 18 ga watan Yulin shekarar da muke ciki ne yan majalisar suka yanke hukuncin bayar da rabin albashin su na watanni 6, don magance matsalolin da talakawa ke ciki.

:::A cikin shekara guda Wike ya rushe gine-gine sama da dubu 20 a Abuja

Mataimakin kakakin majalisar Benjamin Kali, ne ya nemi hakan don magance matsalar zanga-zangar kin jinin mummunan shugabanci da aka gudanar a baya.

Kalu, yace a kowanne wata ana bawa yan majalisar albashin naira dubu dari 6, saboda haka zasu yi watanni 6, suna karbar rabin albashin yayin da za’a bawa talakawa kudaden ta hanyar rage musu azabar da suke ciki.

A yau alhamis kakakin majalisar Tajuddin Abbas, ya sanar da yan uwansa mambobin majalisa cewa kawo yanzu sun tattara adadin naira miliyan N704.91, kuma za’a mikawa shugaban kasa a ranar karshe ta wannan shekara don yiwa al’umma hidima dasu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here