Tinubu ba zai cika alkawarin dake cikin kasafin shekarar 2025 ba—PDP

0
73

Jam’iyyar adawa ta PDP tace ko kadan babu gaskiya a cikin kunshin kasafin kudin shekarar 2025 wanda shugaban Nigeria Bola Tinubu, ya gabatarwa majalisun dokokin kasa a jiya Laraba.

PDP tace a cikin kasafin kudin an tanadi wasu abubuwan da ka’iya sake jefa Nigeria da talakawa cikin kunci da tsadar rayuwa, kamar sakataren yaÉ—a labaran jam’iyyar Debo Ologunagba, ya sanar a cikin wata sanarwa.

Bayan haka PDP tace kasafin zai kara dagula al’amuran tsaro wanda Tinubu, yace an ware masa kaso mafi tsoka a kunshin kasafin.

Tinubu ya gabatar da kasafin na 2025, na naira tiriliyan 47.9 ga majalisun dokoki, inda ya sha alwashin bayar da fifiko ga ɓangaren da samar da tsaro ayyukan raya ƙasa da fannin kiwon lafiya da kuma ilimi.

Sai dai jam’iyyar PDP ta ce gabatar da kasafin kuÉ—in ba wani abu bane illa alÆ™awurran da ba za a iya cikawa ba.

A cikin kasafin an tsara cewa za’a rage yawan hauhawar farashin kayan masarufi zuwa kaso 15 wanda a yanzu haka yake akan kaso 34, cikin dari da ake ganin hakan ba abu ne mai yiwuwa ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here