An sace wayar salula miliyan 25 cikin watanni 12 a Nigeria

0
70

Hukumar kididdiga ta kasa NBS tace an sace wayar tafi da gidanka wadda aka fi sani da GSM, guda miliyan 25 a tsakanin watan Marin na shekarar 2023 zuwa Afrilun 2024.

Cikin wani rahoto da NBS ta fitar na karshen shekara dangane da sace sace, tace akalla mutane miliyan 17, ne aka sacewa wayoyin a wannan tsakani.

Bisa dukkan alamu NBS ta fitar da rahoton hakan bisa la’akari da irin rahotannin sace wayar da al’umma ke kaiwa jami’an yan sanda in hakan ta faru dasu.

Binciken ya nuna cewa a guraren taruwar al’umma aka fi samun sace sacen.

NBS tace mafi yawancin wasu da aka sacewa wayar basu kai rahoto ga jamia’an tsaro ba, wanda haka ya tabbatar da cewa an saci wayar da tafi wannan adadi da aka bayyana in har za’a samu daukacin bayanan wadanda aka sacewa wayar.

Matsalar satar waya ko kwacen ta, na daga cikin manyan lafukan da aka fi aikatawa a wannan lokaci.

A wasu jihohin da suka kunshi Kano da Bauchi, ana yawan samun sata da kwacen waya, wani lokacin har takai ga kashe wanda aka kwacewa wayar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here