Nigeria zata biya bashin naira triliyan 15 a kasafin kudin ta na triliyan 47.9

0
67

Gwamnatin tarayya ta sanar da shirin ta na biyan bashin da ake binta na naira triliyan 15.81, a cikin kasafin kudin ta shekarar 2025, wanda ya kai naira triliyan 47.9.

Shugaban kasa Bola Tinubu, ya bayyana hakan a yau yayin da yake gabatarwa da majalisun dokokin kasa kasafin kudin, yana mai cewa fannin tsaro shine ya samu kaso mafi yawa a cikin kasafin wanda ya tashi da naira triliyan 4.91 sai ayyuka da aka warewa naira triliyan 4.06, ilimi yana biye musu baya da triliyan 3.5.

:::Fannin tsaro da ilimi zasu lashe naira triliyan 8 a kasafin shekarar 2025

Shugaban kasar yace ana sa ran samun kudin shigar da yawan su yakai naira triliyan 34.8, a kasafin na tiliyan kusan 48, wanda za’a cike gibin sa da rancen naira triliyan 13.

Bayan haka kasafin ya tanadi rage hauhawar farashin kayan masarufi daga kaso 34.3, zuwa kaso 15, sai canjin dala da aka tsara zai sauka daga 1700 zuwa 1400 kan kowacce dala guda daya a cikin shekarar ta 2025.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here