Gwamnatin tarayya zata gina sabbin tashoshin lantarki 5

0
73

Gwamnatin tarayya ta amince da shirin samar da sabbin tashoshin wutar lantarki a Sokoto da Onitsha da Abeokuta da offa da kuma Ayede.

Majalisar Zartarwa ta kasa ce ta amince da kashe Naira biliyan N262.75 domin gina tashoshin.

Sabbin tashoshin lantarkin zasu samar da wuta mai ƙarfin 330/132 KV da kuma 132/33 KV.

Ministan Lantarki Adebayo Adelabu, ya sanar da manema labarai hakan, bayan kammala taron majalisar a ranar Litinin.

A cewar sa aikin ya ƙunshi gine-gine da sayen na’urori da kuma hada su, wanda aka ba wa kamfanin Siemens na ƙasar Jamus kwangilar aikin.

Adelabu ya ce za a gina sababbin tashoshin ne domin inganta samar da wutar lantarki a Nigeria.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here