Tinubu ya jagoranci taron kungiyar ECOWAS a birnin Abuja

0
20

Shugabannin Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika (ECOWAS) sun gudanar da wani taro jim kaɗan bayan ficewar ƙasashen Burkina Faso da Mali da kuma Nijar daga kungiyar.

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ne ya jagoranci taron a fadar sa dake birnin tarayya Abuja.

Bisa dukkan alamu taron ya mayar da hankali akan yadda mambobin kungiyar zasu inganta harkokin cigaban tattalin arzikin su, musamman a yanzu da kasashen duniya suka shiga tabarbarewar tattalin arziki.

An kuma tattauna kan tasirin ficewar ƙasashen uku daga kungiyar da kuma sake nazari kan takunkuman da kungiyar ECOWAS ta sanya musu tun a baya, da kuma batun matsalar ta’addanci da ke addabar yankin Sahel.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here