Rikicin PDP: Karin wasu jiga-jigai sun yaudari Atiku, sun koma bayan Wike 

0
149

Wasu gwamnonin PDP da jiga-jigan jam’iyyar musamman daga yankin kudancin Najeriya sun ce lallai idan ana son yin adalci babu yadda za a yi yankin arewacin kasar ya rike tikitin shugaban kasa da kuma mukamin shugaban jam’iyya na kasa.

Masu jagorantar fafutukar ganin Ayu wanda ya fito daga arewa ta tsakiya ya yi murabus, sune Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas da wasu shugabannin jam’iyyar daga kudancin Najeriya.

Hakazalika, a ranar 17 ga watan Satumba, Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo da wasu shugabannin PDP a kudu maso yamma sun yi kira ga murabus din Ayu a taron masu ruwa da tsaki na yankin da suka yi da Atiku.

A wata sanarwa dauke da sa hannun shugabannin kungiyar, Banji Okunomo da Gani Taofik a Lagas a ranar Alhamis, kungiyar ta nuna goyon bayanta ga kira da ake yi na shugaban jam’iyyar yayi murabus, Vanguard ta rawaito.

“Shakka babu yan Najeriya na jiran PDP a matsayin madadin gwamnati, kuma Allah ya kiyaye, idan wannan dama ta wuce mu, ‘yan Najeriya ba za su sake hulda da PDP ba.’

“Muna kira da a gaggauta dawo da kwarin gwiwa hadin kai a cikin Jam’iyyar.”