Gwamnan Bauchi ya nada sabon sakataren gwamnatin jihar

0
57

Sakataren gwamnatin jihar Bauchi, Barista Ibrahim Kashim, ya sauka daga mukamin sa.

Bayanin ajiye mukamin ya fito cikin wata sanarwa da aka fitar daga fadar gwamnatin Bauchi, dauke da sanya hannu mai bai wa gwamnan shawara na musamman kan harkokin yaÉ—a labarai, Muktar Gidado, daya fitar da sanarwar a jiya juma’a.

Sanarwar ta ƙara da cewa gwamnan jihar Bala Mohammed ya amince da murabus ɗin sakataren gwamnatin nasa, tare da gode masa bisa aikin da ya yi da gwamnatinsa.

Tuni Gwamna ya nada shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jihar, Dakta. Aminu Gamawa, ya rike mukamin a matsayin Mukaddashin sakataren gwamnatin jihar ta Bauchi.

Kawo yanzu babu wani abu da aka bayyana a matsala dalilin ajiye aikin da barista yayi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here