Gwamnonin Nigeria sun tattauna akan kudirin dokar haraji

0
49

Gwamnonin kasar nan sun gudanar da wani taro a shalkwatar kungiyar gwamnonin dake birnin tarayya Abuja a cikin daren ranar alhamis da muke ciki, tare da tattaunawa kan batutuwa da dama ciki har da batun sabuwar dokar harajin shugaban kasa Tinubu.

:::Rikici ya kunno kai tsakanin Shugaban karamar hukumar Gwale da daraktan gudanarwar sa

Kawo yanzu babu cikakken bayani akan yadda abubuwa suka kasance yayin taron amma rahotanni daga mabanbantan kafofin yada labarai sun shaida cewa batun kudirin haraji shine makasudin yin taron.

Gwamnonin jami’yyar APC mai mulki 15 ne suka halarci zaman sai gwamnonin biyu da suka fito daga jamiyyar APGA da LP.

Ƙudirin dokar harajin wanda shugaban Najeriya Bola Tinubu ya gabatar wa majalisar dokoki ya janyo suka da ƙorafi daga masu ruwa da tsaki, ciki har da gwamnoni ƙarƙashin majalisar ƙoli ta tattalin arziki, da gwamnoni da ƴan majalisa daga yankin arewa da sai kuma ƙungiyoyi da dama.

Zuwa yanzu majalisar dattawa tayi karatu na biyu akan kudirin, wanda a yanzu ta jingine tattunawa akan sa don bawa wani kwamitin dokar damar tattaunawa da fannin shari’ah akan dokar kamar yadda shugaba Tinubu ya nema.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here