Majalisa ta nemi CBN ya gaggauta magance matsalar karancin takardun kudi

0
32

Majalisar wakilai ta Nigeria ta nuna rashin jin dadin ta akan yadda ake fuskantar karancin takardun kudi a daukacin bankunan kasuwanci na kasar, tare da neman bankin kasa CBN ya magance kalubalen.

Majalisar tace kamata yayi a magance matsalar saboda a fitar da yan kasa daga kuncin rashin kudin.

Wahalar da kudin keyi tasa mutane basa samun su a bankuna sai dai wajen masu Sana’ar POS da su kuma suke zabga caji idan mutum yana neman tsabar Kudin a wajen su.

Kafin yanzu masu sana’ar POS suna cajar naira 100 akan kowacce dubu 10 da suka bayar amma yanzu sun ninka kudin cajin zuwa 200 ko sama da haka akan kowacce dubu 10.

Haka zalika masu kananun sana’o’i suna dandana kudar su saboda rashin tsabar Kudin da hakan ke barazana ga cigaban al’amuran kasuwancin su.

A yanzu haka al’ummar Najeriya na kara fuskantar wahala wajen samun takardar kudi domin harkokin yau da kullum musamman a kauyuka.

Mun ji ta bakin wani mai hada hadar kudi da bankuna a jihar Kano mai suna Muhammad Sani, inda ya shaida mana cewa ya je neman kudi a banki amma bai samu ba, haka ne yasa aka tura masa kudin zuwa wani asusun da shi Kuma ya bashi matsalar da yasha wahala kafin yin amfani da kudin.

Yana da muhimmanci gwamnati ta kawo karshen wannan matsala sakamakon tabarbarewar al’amura da ake ciki wanda hakan ka’iya ta’azara lalacewar tattalin arzikin daidaikun mutane.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here