Kotu ta tura Yahaya Bello Gidan Gyaran Hali na Kuje

0
73

Wata babbar kotun tararyya ta bayar da umarnin tsare tsohon gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello, a gidan gyaran hali na Kuje dake birnin tarayya Abuja.

Kotun tace za’a cigaba da tsare shi har ranar 25 ga watan Fabrairun shekara mai kamawa don cigaba da shari’ar da EFCC ta gurfanar dashi.

:::Hatsarin mota yayi sanadiyyar rasuwar mutane 14 a Jigawa

Indan za’a iya tunawa a dazu mun baku labarin cewa wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta hana belin tsohon gwamnan jihar Kogi Yahya Bello, da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC, ta gurfanar.

Tsohon gwamnan na jihar Kogi ya bayyana a gaban kotun yau Talata, domin neman beli kan shari’ar da ake yi masa ta zargin almundahana da wawure dukiyar jihar sa lokacin da yake Mulki.

A cewar EFCC ana zargin sa da cin kuÉ—in haram da suka haura naira biliyan 100 wanda ya karkata lokacin yana gwamna.

Da take yanke hukunci, mai shari’a Maryanne Anenih, ta ce an gurfanar da Bello ranar 27 ga watan Nuwamba, bayan da jami’ai suka kama shi ranar 26 ga watan.

Sai dai an buƙaci belinsa ranar 22 ga watan na Nuwamba, kwanaki da dama kafin ma ya gurfana.

Mai shari’ar ta ce ya kamata a bukaci beli ne bayan an gurfanar da wanda ake ƙara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here