Yan ta’adda sun sace yara da mata a jihar Zamfara

0
67

Yan ta’addan da suka addabi jihar Zamfara sun kai mummunan hari kauyen Gidan Maidanko na karamar hukumar Maradun, da hakan yasa mutane maza da mata yin gudun tsira da rayuwar su.

Yayin harin yan ta’addan sun sace mutane fiye da 50 dake zaune a yankin.

Bayanai sun nuna cewa maharan ɗauke da muggan makamai sun shiga garin a ranar Asabar da misalin ƙarfe 9:00 na dare.

Wasu mazauna kauyen Gidan Maidanko sun bayyanawa BBC cewa maharan sun sace aÆ™alla mutum 50 zuwa 55, waÉ—anda mafi yawansu mata ne da Æ™ananan yara, amma ba’a sanar da asarar rayuka a harin ba.

Kawo wannan lokaci yan ta’addan da suka yi wannan mummunan aiki basu tuntubi iyalan mutanen da suka sace.

Zuwa yanzu hukumomi ba su ce komai ba game da lamarin. Kakakin rundunar ‘yansanda a Zamfara, Yazid Abubakar, ya ce yana kan wani aiki, yayin da Kwamashinan ‘Yansanda Muhammed Shehu Dalijan bai dawo da kiran waya da aka yi masa ba.

Garin na Gidan Maidanko na da nisan kilomita kusan 92 daga Gusau babban birnin jihar Zamfara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here