Hisbah ta kara jan hankalin al’umma su dena janyo fushin Ubangiji

0
56

Rundunar Hisbah ta jihar Kano ta kara jan hankalin al’umma da su dena janyo fushin Ubangiji, da hakan ke haifar da mummunar makoma a duniya da lahira.

Mataimakin babban kwamandan Hisbah Dr Mujahiddin Aminudden, ne ya sanar da hakan lokacin da jami’an su ke rangadin atisayen gyara kayan ka, da rundunar Hisbah ke yin amfani da fasaha wajen janyo hankalin masu aikata laifuka su tuba su koma ga Allah.

Dr. Mujahiddin Aminudden, yace a jiya jami’an Hisbah sun kai ziyara wuraren taruwar matasa da ka’iya aikata sabon Allah inda aka yi musu wa’azi da nuna musu gaskiya.

Wuraren da aka je sun kunshi, Banana, Miyangu, Race course, Tukur Road, Ahmadu Bello way, Danna Gari, da sauran su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here