Ya kamata asibitoci su kiyaye da sabon nau’in Cutar Corona—Gwamnatin tarayya

0
80

Gwamnatin tarayyar Nigeria ta ankarar da daukacin mahukuntan asibitocin kasar cewa akwai bukatar tsaurara matakan gano sabon nau’in cutar Corona mai suna XEC COVID-19, da kuma bayar da rahoto kan cutar, da tuni ta bulla a kasar Australia.

Cikin wata takarda da ma’aikatar lafiya ta Nigeria ta fitar zuwa ga daukacin shugabannin asibitoci, ta nemi a tsaurara matakan kariya daga kamuwa da cutar da kuma bin diddigin gano sabon nau’in cutar.

Takardar da ma’aikatar lafiyar ta fitar tace zuwa yanzu cutar XEC COVID-19, ta shiga kasashe 29, bayan fara bullar ta daga kasar Australia, inda sanarwar tace nau’in cutar yana da sauri wajen yaduwa a tsakanin al’umma, da hakan ya haifar da damuwa musamman yanda hakan ke da tasiri ga tsarin kula da lafiyar mutane.

Shugaban sashin kula da asibitocin koyarwa na ma’aikatar lafiya Dr. O.N. Anuma, ne ya sanar da hakan cikin takardar daya sakawa hannu, sannan ya umarci ayi duba na tsanaki ga marasa lafiyar da suke nuna irin alamun kamuwa da cutar ta XEC COVID-19.
Idan za’a iya tunawa an fara samun cutar coronavirus a shekarar 2019,da aka gano a birnin Wuhan, na kasar China.
A wancan lokaci cutar ta zama babbar annoba ga duniya musamman yanda ta zama sanadiyyar mutuwar mutane da yawa, har ma da karyewar tattalin arzikin kasashen duniya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here