Gwamnatin Kano tayi ala Wadai ta girke jami’an tsaro a Masarautar Kano

0
33

Gwamnatin Kano ta mayar da martani kan yadda aka wayi gari da ganin dimbin jami’an tsaro a fadar masarautar Kano, tare da hana Sarkin Kano Muhammadu Sunusi na II, halartar nadin sarautar hakimin Bichi.

Gwamnatin ta mayar da martanin ta bakin sakataren ta Dr. Baffa Bichi, wanda yayi ala wadai da abun da jami’an tsaron suka yi.

Baffa Bichi, ya bayyanawa kafar yada labarai ta Freedom Radio, cewa gwamnatin tarayya suke zato da bayar da umarnin yin hakan, yana mai cewa wani yunkuri ne ake yi na tayar da tarzoma a Kano.

A cewar sa koda suka nemi jin ta bakin jami’an tsaron sun ce umarni aka basu daga sama cewa su rufe mashigar masarautar Kano da fadar Bichi.

Idan zaku iya tunawa mun baku labarin cewa, Jami’an da suka je fadar Sarkin na Kano, sun kunshi yan sanda, da jami’an tsaro na farin kaya.

Fadar masarautar Kano, nan ne inda Sarkin Kano na Muhammadu Sunusi, na II yake zaune.

Rahotanni sun bayyana cewa jami’an tsaron sun hana mai martaba sarki Muhammadu Sunusi, yin zaman fada na yau juma’a, da kuma halartar wani taro a karamar hukumar Bichi, wanda aka tsara gudanarwa a wannan rana.

Wata Majiya daga masarautar Kano, ta shaidawa Jaridar News Point, cewa zuwan jami’an tsaron baya rasa nasaba da taron kaddamar da hakimin karamar hukumar Bichi, da Sarkin Muhammadu Sunusi zai yi, a karamar hukumar ta Bichi.

Haka zalika, majiyar tace an umarci Sarkin Muhammadu Sunusi, ya cigaba da kasancewa a cikin gidan masarautar, yayin da jami’an tsaro dauke da kayan aiki ke kofar gidan

Bayan haka, majiyar ta kara da cewa Mai martaba sarki Muhammadu Sunusi na II, ya kira waya don sanin abinda yasa aka jibge wa masarautar yan sandan.

Wata majiyar kuma daga gwamnatin Kano, tace gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya aike da wata tawagar zuwa masarautar Kano don jin abinda ke faruwa sai dai jami’an tsaron sun hana su damar shiga gidan masarautar.

Zuwa yanzu an samu bayanin cewa a can karamar hukumar ta Bichi, ma an zuba jami’an tsaro a wajen da aka tsara yin taron kaddamar da hakimin na Bichi.

Wannan dambarwa dai bata rasa nasaba da rikicin nadin sarautar da aka yiwa Muhammadu Sunusi na II, bayan cire Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero, sannan aka rushe masarautun Kano guda hudu, na Bichi, Rano, Karaye da Gaya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here