Bama bamai uku sun fashe a jihar Zamfara

0
39

Akalla abubuwan fashewa uku ne suka tarwatse a mabanbantan gurare a garin Dansadau na karamar hukumar Maru dake jihar Zamfara.

Jaridar Premium Times, ta rawaito cewa abubuwan sun fashe a garuruwan Dansadau, Malamawa da Malele duk a garin na Dansadau.

Wani mazaunin garin mai suna Nuhu Babangida, yace wasu fasinjojin babbar mota sun tsallake rijiya da baya sakamakon kaucewa taka nakiyar bom din da aka binne a hanyar su ta zuwa cin kasuwar mako mako a yau juma’a.

Babangida, yace bama baman sun tashi a Malamawa da Malele, amma ba’a samu asarar rayuka ba.

Bom na uku ya tashi akan hanyar Dansadau, bayan an saka shi akan hanya.

A wannan lokaci dai ana samun karuwar ayyukan ta’addanci a yankin Dansadau, dake jihar Zamfara, wanda a ranar laraba mutane 12, suka mutu sakamakon fashewar Bom a yankin Yar Tasha.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here