Majalisar dokikin Kano tayi watsi da dokar harajin shugaba Tinubu

0
50

Majalisar dokikin Kano tayi watsi da dokar harajin shugaba Tinubu, da a halin yanzu take gaban majalisun dokokin kasa don neman amincewa, yayin da majalisar ta Kano ke kafa hujja da cewa dokar harajin zata kasance mai mummunan tasiri ga arewa.

:::Ba dokar haraji ce tasa aka dauke daurin auren iyalan Barau daga Kano ba—Iyalan Ado Bayero

Majalisar ta Kano ta dauki wannan mataki a zaman ta na jiya, wanda kakakin ta Hon. Ismail Jibrin Falgore, ya jagoranta.

Shugaban masu rinjaye na majalisar Lawan Hussaini, ne ya gabatar da kudirin neman yin watsi da dokar, sannan ya nemi sauran yan majalisun dokokin arewa su kauracewa amincewa da waccan dokar haraji.

Yace tabbas akwai son cutar da arewa a cikin dokar, inda ya kara da cewa dokar zata kara jefa mutanen arewa cikin kuncin rayuwa.

Lawan Hussaini, yace jihar Lagos, ce zata amfani dokar saboda yawan kamfanonin da take dasu, a daidai lokacin da jihohin arewa ke fuskantar kalubalen biyan albashin ma’aikata.

Shima dan majalisar mai wakiltar Doguwa, Salisu Muhammad Doguwa, ya goyi bayan kudirn da Lawan Hussaini, ya gabatar yana mai neman majalisar dattawa ta mayar da hankali akan kalubalen tsaro, rashin aikin yi, bawai gaggawar amincewa da dokar haraji ba.

Daga karshe dai majalisar ta Kano, ta yanke hukuncin kin goyon bayan dokar tare da rokon sauran yan majalisar arewa su kalubalance ta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here