ASUU za ta daukaka kara kan umarnin Kotu na janye yajin aikinta

0
124

Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya ASUU ta shirya daukaka kara kan umarnin da kotun masana’antu ta bata na dakatar da yajin aikin da ta kwashe watanni Bakwai tana yi.

A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar shiyyar Lagos, Mr Adelaja Odukoya, yace kungiyar ta bukaci Yayanta da su kwantar da hankalinsu akan umarnin Kotun Kuma su jira mataki na gaba

Kungiyar ta ce tuni lauyanta ya shigar da kara akokarin bin kadin wannan umarni.

Sanarwar tace; “Ku kwantar da hankalinku.” Ta kuma bukaci mambobin kungiyar da ‘yan Najeriya da su kasance masu hadin kai, duk da cewa za a janye wannan umarni.

Sanarwar ta kara da cewa; “Shugaban kungiyarmu, Kwamared Victor Osodeke, ya bukaci mambobin kungiyarmu ta kasa da su kwantar da hankalinsu domin babu wani abin damuwa a bayan aiki da aka gabatar a yau.

“Lauyan mu ya shigar da kara dan dakatar da aiwatar da wannan hukuncin. Ba za a taɓa yin galaba a kan jama’ar da ke haɗin kai ba tare da sulhu ba.