Gwamnatin Kano Tana Sake Gina Hasumiyar data Rusa

0
58

A watannin baya ne Gwamnatin jihar Kano, karkashin Engr Abba Kabir Yusuf, ta rushe babbar hasumayar shataletalen gaban gidan jihar, wanda tsohuwar gwamnatin Ganduje ta samar bayan kashe mata makudan kudade wajen gina ta.

A yayin rushewar gwamnatin Kano ta kafa hujja da cewa hasumayar dana dauke da alamar Cross a Samanta, tare da cewa zata iya kawowa gidan gwamnatin barazanar tsaro.

Sai dai a yanzu haka Mai girma Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya bayar da umarnin sake gina hasumayar a dandalin Shari’a dake Kofar Nassarawa da za’a kashe naira miliyan 164.9, wajen sake ginin.

Bayan haka itama Hasumiyar Dandalin Shari’ar za’a matsar da ita gefe kadan kusa da katangar jami’ar Northwest Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here