Bamu shirya yin takara a shekarar 2027 ba—–Atiku, Obi

0
105

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP, Peter Obi, sun musanta zargin tattaunawa a tsakanin su don takarar shugabancin kasa a shekarar 2027.

An karade kafafen sada zumunta da jita jitar cewa Atiku da Obi, sun zanta dangane da batun yanda zasu bullowa takarar shugabancin Nigeria a shekarar 2027.

Wannan zargi ya biyo bayan yadda aka gano hoton Atiku Abubakar da Peter Obi suna yin karin kumallo lokacin da Obi, ya kaiwa Atiku ziyara a mahaifiyar sa ta Adamawa.

Atiku Abubakar, shine ya yada hotunan ziyarar da Obi, yakai masa tare da saka hotunan a shafin sa na X a ranar asabar data gabata, sannan ya rubuta cewa munyi karin kumallo tare da abokina Peter Obi a jihar Adamawa.

Sai dai mai taimakawa Peter Obi, a fannin kafafen yada labarai Ibrahim Umar, yace ba maganar siyasar 2027, ce tasa manyan yan siyasar ganawa a wannan lokaci ba.

A kwanakin baya ma an yada cewa Atiku Abubakar, Peter Obi, da Rabi’u Musa Kwankwaso, suna da sha’awar hada kai don kifar da Gwamnatin Tinubu, a shekarar 2027.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here