Bazan saurarawa sauyin tattalin arzikin dana faro ba—Tinubu

0
60

Shugaban Nigeria Bola Ahmed Tinubu, tabbatar da cewa gwamnatin zata cigaba da daukar matakan da take ganin sun dace akan sauyin tattalin arzikin kasar, yana mai cewa manufar sa zata samar da cigaban nahiyar Africa baki daya.

Shugaban ya bayyana hakan lokacin da yake zantawa da shugaban Faransa Emmanuel Macron, sannan yace babu gudu babu ja da baya akan manufofin sa a Nigeria.

Da yake jawabi a wajen liyafar cin abincin dare da gwamnatin Faransa ta shirya masa a fadar gwamnatin Faransa ta Palais des Elysée da ke birnin Paris a daren Alhamis, Tinubu ya ƙarfafa gwiwar ‘yan Najeriya da Faransa da su ci gaba da ƙulla kyakkyawar alaƙar da ƙasashen ke yi.

Tinubu ya ce Afirka ba ta da wani zaɓi illa gina nahiyar da za ta bunƙasa fannoni da dama da suka kamata, da kuma inganta shirin walwalar jama’arta.

A nasa jawabin, Shugaban Faransa Macron ya yaba da shugabancin Najeriya a nahiyar Afirka, musamman dangane da rawar da take takawa a matsayin jigon nahiyar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here