Hisbah ta kama masu sayar da Giya a kauyukan Jihar Kano

0
68

Rundunar Hisbah ta jihar Kano ta samu nasarar kama wani mutum mai suna Francis, wanda ya kware wajen cinikayyar giya, wadda shan ta ya haramta bisa dokokin addinin muslinci, da tanadin hukumar Hisbah ta Kano.

Mataimakin babban kwamandan rundunar Dr Mujahiddin Aminudden, ne ya sanar da kama mutunin a kwanar Dangora, wanda yake siyan giya don kaiwa kauyen Daka tsalle.

Dr Mujahiddin yace, dakarun Hisbah sun jima suna kokarin kama mai laifin, tun ba yau ba, wanda sai yanzu Allah ya basu nasarar kama Francis, Kuma za’a mika shi gaban kotu don hukunta shi.

An same shi tare da Direban motar dakon giyar fiye da katan 80.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here