Ngozi Okonjo-Iweala, ta sake zama shugabar hukumar kasuwanci ta duniya

0
62

Haifaffiyar Nigeria, masaniya akan harkokin tattalin arziki da kasuwanci Ngozi Okonjo-Iweala, ta sake zama shugabar hukumar kasuwanci ta duniya a karo na biyu.

Ngozi, itace mace ta farko data taba rike wannan mukami, sannan itace yar Afrika data rike mukamin na Hukumar WTO, a karon farko.

Ta samu nasarar sake zama shugabar hukumar, bayan rashin samun wani da zai yi takara da ita bayan karewar wa’adin shugabancin ta a hukumar.

Haka ne yasa mambobin hukumar su 166, suka amince Ngozi Okonjo, ta cigaba da rike mukamin a sanarwar da suka fitar yau juma’a.

Sanarwar tace Ngozi Okonjo, mai shekaru 70, a duniya ta sake samun mukamin bayan taron sirri da mambobin WTO, suka gudanar, sakamakon cewa wa’adin ta na farko zai kare karshen watan Ogusta na 2025.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here