Babu gaskiya a fara aikin matatar mai ta Fatakwal–Al’ummar Alesa

0
82

Kamfanin mai na Nigeria NNPCL, ya musanta ikirarin da wasu al’ummar Alesa suka yi na cewa NNPCL, ya yiwa yan Nigeria karya akan batun fara tace fetur da akace matatar Fatakwal ta fara a wannan makon.

Idan za’a iya tunawa a ranar alhamis data gabata ne, Timothy Mgbere, wanda yake a matsayin jagoran al’ummar Alesa, ya bayyana a kafar talbijin ta kasa NTA, tare da cewa kamfanin NNPCL karya yake zubawa yan Nigeria, akan cewa an fara tace fetur a Fatakwal, yana mai cewa ko kadan babu wannan zance, Kuma babu aikin da akeyi a matatar.

Sai dai safiyar yau juma’a mai magana da yawun kamfanin NNPCL, Olufemi Soneye, ya yi watsi da kalaman Mgbere, inda yace mai yin zargin bai san komai akan harkokin matatar mai ba, Kuma ba gaskiya yake fada ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here