Majalisar wakilai ta tabbatar da Olufemi Oluyede a matsayin babban hafsan sojin kasa

0
44

Majalisar wakilai ta tabbatar da Olufemi Oluyede, a matsayin babban hafsan sojin kasa, na Nigeria.

Amincewa nadin nasa yazo a bayan tantance shi da kwamitin majalisar akan harkokin tsaro da sojoji yayi a jiya laraba.

:::Kudirin dokar haraji ya tsallake karatu na biyu a majalisar dattawa

Shugaban kwamitin Babajimi Benson, ne ya mikawa majalisar rahoton tantancewar, tare da rokon majalisar ta tabbatar da Laftanar Janar Olufemi Oluyede, a matsayin.

Mataimakin kakakin majalisar Benjamin Kalu, da ya jagoranci zaman na yau wanda kuma shine ya tabbatar da Olufemi Oluyede, a matsayin babban hafsan sojojin kasa, na Nigeria.

Shugaban kasa Bola Tinubu, ne ya nemi majalisar ta amince da nadin Olufemi Oluyede, sakamakon mutuwar tsohon babban hafsan Taoreed Lagbaja, a kwanaki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here