Za’a yi kidayar al’ummar Nigeria a shekarar 2025

0
53

Shugaban hukumar kidaya ta kasa NPC, Nasir Isa Kwarra, ya sanar da cewa zasu gudanar da kidayar al’ummar Nigeria a cikin shekara mai kamawa ta 2025.

Kwarra, ya bayyana hakan a yau lokacin da yake jawabi a taron kasa da kasa na cigaban yawan al’umma dake gudana a birnin tarayya Abuja.

Idan za’a iya tunawa majalisar dinkin duniya, ta bayar da shawarar gudanar da kidayar al’umma a kowacce kasa bayan kowacce shekara 10, amma hakan ya gagara a Nigeria, sakamakon cewa tun shekarar 2006, ba’a sake gudanar da kidayar al’umma a Nigeria ba.

A ka’ida za’a gudanar da kidayar a shekarar 2023, amma ba’a yi ba, bayan saka lokacin gudanar da kidayar har sau biyu a karkashin gwamnatin tsohon shugaban Nigeria Buhari.

Gwamnatin Buhari, ta janye gudanar da kidayar a wancan lokaci don bawa sabuwar gwamnatin da zata zo a bayan ta damar shirya kidayar.

Nasir Kwarra, yace wasu kalubalen da suka shafi kudi na daga cikin matsalolin da suka hana aiwatar da shirin kidayar a shekarar 2023.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here