Yau ake cika shekaru 10 da kai harin Boko Haram na Masallacin masarautar Kano

0
100

A yau 28 ga watan Nuwamba ake cika shekaru 10 cif da Kungiyar Boko Haram, ta kai mummunan harin daya tayar da hankalin al’ummar Jihar Kano, arewacin Nigeria, da ma kasar baki daya a ranar 28 ga watan Nuwamba na shekarar 2014.

An kai harin ne zuwa masallacin Juma’a dake gidan Sarkin Kano, wanda yake tara mutane da yawa domin yin Sallah.

Harin ya faru ana tsaka da gudanar da Sallar juma’a a wannan rana inda mayakan boko haram masu kunar bakin wake suka tayar da bama-bamai, tare da bude wuta akan masallata, hakan ne ya sanya aka samu mutuwar mutane da ba’a taba fuskanta ba a jihar Kano a lokaci guda.

Rahotanni sun bayyana cewa an samu mutuwar akalla mutane 300, bayan wadanda suka ji munanan raunukan da suka nasaka.

A wannan lokaci an fuskanci tashin hankali da ba’a taba fuskantar irin sa ba.

Asibitocin kwaryar birnin Kano, sun cika da marasa lafiya, inda al’umma suka rika kai kansu domin bayar da gudunmuwar jini don sakawa mutanen da harin ya rutsa dasu.

Daga wancan lokaci ba’a sake samun kai hari Masallacin juma’a a jihar Kano ba, sakamakon addu’a da aka bawa muhimmanci da kuma daukar matakan kariya da al’umma suka fara yi.

Muna fatan Allah ya gafartawa wadanda suka rasu, ya kiyaye afkuwar hakan a nan gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here