Kungiyar ASUP zata shiga yajin aiki a farkon Disamba

0
126

Shugaban kungiyar makarantun kimiyya da fasaha, ta Kasa ASUP reshen jihar Kaduna Kwamared Abubakar J. Abdullahi, yace za’a rufe makarantun kimiyya da fasaha dake fadin Nigeria tare da tsunduma yajin aiki saboda gazawar gwamnatin tarayya wajen biyan bukatun kungiyar daga ranar 2 ga watan Disamba na wannnan shekara.

Yace tun a ranar 6 ga watan Oktoba, kungiyar ta bawa gwamnati wa’adin kwanaki 15 data kula da biyan bukatun su na magance wasu matsalolin da kwalejojin ke fuskanta da suka hana su cigaba, sai dai har kawo wannan lokacin babu wani bayani da gwanatin tayi ko daukar mataki.

Lokacin da yake yin karin haske ga manema labarai a ranar talata Kwamared Abubakar J. Abdullahi, yace bukatun su sun hadar da aiwatar da karin albashin kaso 25 zuwa 35 a albashin ma’aikatan dake karkashin ASUP, da kuma biyan malaman karin wasu hakkin su da gwamnatin ta gaza biya

Kwamared Abubakar J. Abdullahi, ya kara da cewa babban abin takaici ne yadda aka cinye wa’adin da suka bawa gwanatin ba tare da ta kalle su ba ballantana daukar wani kwakkwaran mataki, yana mai cewa daga haka basu da wani zabi daya wuce shiga yajin aiki.

A cewar sa ilimi shine ginshikin kowacce al’umma sai dai duk da haka gwamnati tana yin wasa da fannin wajen rashin bawa ilimi kulawar data dace, sannan ya roki gwamnati data zauna da yan kungiyar ASUP, don samar da afita kan matsalolin da yayan kungiyar ke ciki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here