Kananun yara fiye da dudu 150 sun kamu da cutar HIV a Nigeria

0
130

Gwamnatin tarayya ta bayyana rashin jin dadin ta danganta da rashin samun cikakkiyar kariya daga kamuwa da cuta mai karya garkuwar jiki wato HIV.

Daraktar hukumar Kula da Cuta Mai Karya Garkuwar Jiki ta Kasa (NACA), Dr. Temitope Ilori, ce ta nuna damuwa akan hakan, inda tace damuwar tafi karfi a bangaren yada cutar zuwa ga jarirai.

Bisa yadda ake bukata ana son rage yiwuwar kamuwar cutar ga jarirai da kaso 95 cikin dari amma hakan baya samuwa sai dai kaso 33, ake samu na dakile bazuwar cutar mai karya garkuwar jiki.

Temitope Ilori, ta ce kimanin yara 160,000 masu shekaru kasa da 14 suna dauke da cutar a Nijeriya kamar yadda rahoton UNAIDS na 2023 ya nuna.

Ta ce Nijeriya na da kashi 1.4 na masu cutar a jikin mutanen da shekarunsu ke tsakanin 15 zuwa 64, tare da mutane miliyan biyu da ke fama da cutar.

A duk shekara, Nijeriya na samun sabbin mutane 22,000 da ke kamuwa da cutar, sai mutane 15,000 da ke mutuwa saboda cututtukan da suka shafi cuta mai karya garkuwar jiki.

Saboda hakan gwamnatin tarayya ta kafa wani kwamitin da zai yi kokarin tabbatar da cewa an dena haifar yara masu kamuwa da cutar HIV.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here